Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 6:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana.

2. Sai goma sha biyun nan suka kirawo duk jama'ar masu bi, suka ce, “Ai, bai kyautu ba mu mu bar wa'azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha'anin abinci.

3. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki.

4. Mu kuwa sai mu nace da yin addu'a da kuma koyar da Maganar.”

Karanta cikakken babi A.m. 6