Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 5:24-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai.

25. Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama'a.”

26. Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.

27. Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su,

28. ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”

29. Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.

30. Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume.

31. Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.

32. Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”

33. Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su.

34. Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.

35. Sa'an nan ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.

36. Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutum arbaminya kuma suka bi shi, amma aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace.

Karanta cikakken babi A.m. 5