Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 28:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sa'ad da Bulus ya tattaro waɗansu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wani maciji ya bullo saboda zafi, ya ɗafe masa a hannu.

4. Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”

5. Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.

6. Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.

7. A nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku.

8. Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu'a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.

9. Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.

10. Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.

11. Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.

12. Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.

13. Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.

14. A nan muka tarar da waɗansu 'yan'uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.

15. Da 'yan'uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.

16. Da muka shiga Roma aka yardar wa Bulus ya je ya sauka abinsa tare da sojan da yake tsaronsa.

Karanta cikakken babi A.m. 28