Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Bayan da muka haye bahar ɗin da yake kusa da kasar Kilikiya da ta Bamfiliya, muka isa Mira ta ƙasar Likiya.

6. A nan jarumin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki.

7. Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan kaɗan, har da ƙyar muka kai kusa da Kinidas. Da dai iska ta hana mu ci gaba, muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni.

8. Muna bin gefen gaɓarsa da ƙyar, har muka isa wani wuri mai suna Amintacciyar Mafaka, wadda take kusa da birnin Lasiya.

9. Da yake an ɓata lokaci mai yawa, tafiyar ma ta riga ta zama mai hatsari, lokacin azumi kuwa ya wuce, sai Bulus ya gargaɗe su,

10. ya ce musu, “Ya ku jama'a, na dai ga tafiyar nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukanmu.”

11. Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa.

12. Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.

13. Da iska ta buso daga kudu sannu sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya ke nan, sai suka janye anka suka bi ta gefen tsibirin Karita gab da gaci.

14. Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin.

15. Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu.

Karanta cikakken babi A.m. 27