Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Saboda hadiri yana sa mu tangaɗi ƙwarai da gaske, kashegari sai suka fara watsar da kayan da jirgin ya ɗauko, a ruwa.

19. A rana ta uku kuma, su da kansu suka jefar da kayan aikin jirgin.

20. Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.

21. Da yake an daɗe ba cin abinci, sai Bulus ya miƙe a tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Ya ku jama'a, da kun ji maganata, da ba ku taso daga tsibirin Karita kun fāɗa wannan masifa da hasara ba.

22. To, a yanzu, ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin.

23. Don a daren jiya wani mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,

24. ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’

25. Saboda haka, sai ku yi ƙarfin hali, ya ku jama'a, domin na gaskata Allah a kan cewa, yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi.

26. Amma fa lalle ne a fyaɗa mu a wani tsibirin.”

27. A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakar dare sai masu tuƙi suka zaci mun yi kusa da ƙasa.

28. Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar.

29. Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye.

30. Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su,

31. sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”

Karanta cikakken babi A.m. 27