Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 26:4-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama'armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukan Yahudawa.

5. Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.

6. Ai, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakanninmu nake nan a tsaye a yi mini shari'a.

7. Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!

8. Yaya cewa Allah yana ta da matattu sa'an nan, ya ƙi gaskatuwa a gare ku?

9. “To, ni kaina ma a dā na ga kamar wajibi ne in yi abubuwa da yawa, na gāba da sunan Yesu Banazare.

10. Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan firstoci, na kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma a lokacin da ake kashe su ina goyon bayan yin haka.

11. Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami'u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”

12. “Cikin halin haka ne, ina tafiya Dimashƙu da izinin manyan firistoci da kuma saƙonsu,

13. da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.

14. Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa a kan tsini.’

15. Ni kuwa sai na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

16. Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.

17. Zan tsirar da kai daga jama'ar nan da kuma al'ummai, waɗanda zan aike ka a gare su,

18. domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”

19. “Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.

Karanta cikakken babi A.m. 26