Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 26:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni a nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku,

23. cewa dai lalle ne Almasihu yă sha wuya, shi ne kuma zai fara tashi daga matattu, ya sanar da jama'ar nan da al'ummai haske.”

24. Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Festas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”

25. Amma Bulus ya ce, “Ya mafifici Festas, ai, ban ruɗe ba, gaskiya nake faɗa, cikin natsuwa kuwa.

26. Ai, al'amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata ba abin da ya kuɓuce wa hankalinsa cikin al'amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.

27. Ya sarki Agaribas, ka gaskata annabawa? Na dai sani ka gaskata.”

28. Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Wato a ɗan wannan taƙaitaccen lokaci kake nufin mai da ni Kirista?”

29. Bulus kuwa ya ce, “Ko a ɗan wannan, ko a mai yawa, ina fata ga Allah, ba kai kaɗai ba, har ma duk waɗanda suke saurarona a yau, su zama kamar yadda nake, sai dai banda sarƙar nan.”

30. Sai sarki ya tashi, haka kuma mai mulki da Barniki, da waɗanda suke a zaune tare da su.

31. Bayan sun keɓe waje ɗaya, suka yi shawara, suka ce, “Ai, mutumin nan bai yi wani abin da ya isa kisa ko ɗauri ba.”

32. Agaribas kuma ya ce wa Festas, “Ba don dai mutumin nan ya riga ya nemi ɗaukaka ƙararsa a gaban Kaisar ba, da sai a sake shi.”

Karanta cikakken babi A.m. 26