Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 24:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama'armu,

3. kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko'ina, tare da godiya ba iyaka.

4. Amma don kada in gajiyad da kai, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.

5. Mun tarar da mutumin nan fitinanne ne, yana ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko'ina a duniya, shi kuma ne turun ɗariƙar Nazarawa.

6. Har ma yana nema ya tozarta Haikali, amma muka kama shi. [Niyyarmu ce mu hukunta shi bisa ga shari'armu.

7. Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu ƙarfi da yaji,

8. ya yi umarni masu ƙararsa su zo a gabanka.] In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarar da muke tāsarwa.”

9. Yahudawa ma suka goyi bayan haka, suna tabbatarwa haka abin yake.

10. Da mai mulki ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce, “Tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama'ar nan shari'a, da farin ciki zan kawo hanzarina.

11. Ai, ka iya tabbatarwa, bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima yin sujada.

12. Ba su kuwa taɓa samuna ina muhawwara da kowa ba, ko kuwa ta da husuma har mutane su taru a Haikali, ko a majami'u, ko kuwa a cikin birni.

Karanta cikakken babi A.m. 24