Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 23:4-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”

5. Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, 'yan'uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama'a.’ ”

6. Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya 'yan'uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari'a.”

7. Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu.

8. Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.

9. Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”

10. Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.

11. Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”

12. Da gari ya waye, Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.

13. Waɗanda suka ƙulla wannan makirci kuwa sun fi mutum arba'in.

14. Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kashe Bulus.

15. Saboda haka, yanzu ku da majalisa ku shaida wa shugaban soja ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso.”

16. To, ɗan 'yar'uwar Bulus ya ji labarin farkon da za su yi, ya kuma je ya shiga kagarar soja ya gaya wa Bulus.

Karanta cikakken babi A.m. 23