Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 20:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.

2. Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,

3. ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.

4. Subataras Babiriye, ɗan Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundas, mutanen Tasalonika, da Gayus Badarbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimas, mutanen Asiya,

5. waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa.

6. Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan idin abinci marar yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna har kwana bakwai.

7. A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura gurasa, Bulus ya yi masu jawabi, don ya yi niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakar dare.

8. Akwai kuwa fitilu da yawa a benen da muka taru.

Karanta cikakken babi A.m. 20