Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 18:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa'azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne.

6. Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.”

7. Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titus Yustus mai ibada, gidansa kuwa gab da majami'a yake.

8. Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.

9. Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi wa Bulus wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa'azi, kada ka yi shiru,

10. domin ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”

11. Sai Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar da Maganar Allah a cikinsu.

12. Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a,

13. suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane, wai su bauta wa Allah ta hanyar da Shari'ar ta hana.”

14. Bulus na shirin yin magana ke nan sai Galiyo ya ce wa Yahudawan, “Ku Yahudawa! Da ma wani laifi ya yi, ko munafunci, da sai in iya sauraronku.

15. Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma shari'arku, ai, sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam, ba ni da niyyar yin shari'a irin waɗannan abubuwa.”

16. Sai ya kore su daga ɗakin shari'a.

17. Sai duk suka kama Sastanisu, shugaban majami'a, suka yi masa dūka a gaban gadon shari'a. Amma Galiyo ko yă kula.

18. Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.

19. Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami'a ya yi muhawwara da Yahudawa.

Karanta cikakken babi A.m. 18