Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 18:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan haka Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Koranti.

2. Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.

3. Da yake kuma sana'arsu ɗaya ce, maɗinkan tanti ne, ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare.

4. Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami'a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al'ummai.

5. Sa'ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa'azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne.

6. Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.”

7. Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titus Yustus mai ibada, gidansa kuwa gab da majami'a yake.

8. Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.

Karanta cikakken babi A.m. 18