Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 17:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da waɗansu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza.

13. Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.

14. Nan da nan kuwa 'yan'uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Sila da Timoti suka dakata a nan.

15. Waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina. Bayan Bulus ya yi musu saƙon umarni zuwa wurin Sila da Timoti, cewa su zo wurinsa da gaggawa, suka tafi.

16. To, sa'ad da Bulus yake dākonsu a Atina, ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko'ina gumaka ne a birnin.

17. A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami'a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.

18. Har wa yau kuma waɗansu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka ci karo da shi. Waɗansu suka ce, “Me wannan mai surutu yake nufi?” Waɗansu kuwa suka ce “Ga alama, mai yin wa'azin bāƙin alloli ne”– domin kawai yana yin bisharar Yesu, da kuma tashi daga matattu.

19. Sai suka riƙe shi suka kai shi Tudun Arasa, suka ce, “Ko ka faɗa mana wace irin baƙuwar koyarwa ce wannan da kake yi?

20. Domin ka kawo mana abin da yake baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma'anarsa.”

Karanta cikakken babi A.m. 17