Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 16:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai wani almajiri a Listira, mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne.

2. Shi kuwa 'yan'uwan da suke Listira da Ikoniya na yabonsa.

3. Sai Bulus ya so Timoti ya rako shi, har ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da suke waɗannan wurare, don duk sun san ubansa Bahelene ne.

4. Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama'a ƙa'idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.

5. Ta haka ikilisiyoyi suka ƙarfafa a cikin bangaskiya, a kowace rana suna ƙara yawa.

6. Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.

7. Da suka zo kan iyakar ƙasar Misiya, sai suka yi ƙoƙarin zuwa ƙasar Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yardar musu ba.

8. Suka kuwa ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa.

9. Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”

10. Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.

11. Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har zuwa tsibirin Samutaraki, kashegari kuma sai Niyabolis,

12. daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi 'yan kwanaki.

Karanta cikakken babi A.m. 16