Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 14:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.

9. Yana sauraron wa'azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,

10. ya ɗaga murya ya ce, “Tashi, ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya.

11. Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Lalle, alloli sun sauko mana da siffar mutane!”

12. Sai suka ce Barnaba shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai shi ne Hamisa.

13. Sai sarkin tsafin Zafsa, wanda ɗakin gunkinsa yake ƙofar gari, ya kawo bajimai da tutocin furanni ƙofar gari, yana son yin hadaya tare da jama'a.

14. Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa,

15. “Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.

16. Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al'ummai su yi yadda suka ga dama.

17. Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”

18. Duk da waɗannan maganganu da ƙyar suka hana jama'ar nan yin hadaya saboda su.

Karanta cikakken babi A.m. 14