Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 12:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa'an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi 'yan kwanaki a can.

20. To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.

21. Ana nan a wata rana da aka shirya, Hirudus ya yi shigar sarauta, ya zauna a gadon sarauta, ya yi musu jawabi.

22. Taron mutane kuwa suka ɗauki sowa, suna cewa, “Kai! ka ji muryar wani Allah, ba ta mutum ba!”

23. Nan take sai mala'ikan Ubangiji ya buge shi don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.

24. Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, tana yaɗuwa.

25. Sai Barnaba da Shawulu suka komo daga Urushalima, bayan sun cika aiken da aka yi musu, suka kuma zo da Yahaya wanda ake kira Markus.

Karanta cikakken babi A.m. 12