Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 10:22-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai suka ce, “Wani jarumi ne, wai shi Karniliyas, mutumin kirki, mai tsoron Allah, wanda duk jama'ar Yahudawa suke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala'ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.”

23. Sai Bitrus ya shigo da su, ya sauke su.Kashegari ya tashi suka tafi tare, waɗansu 'yan'uwa kuma daga Yafa suka raka shi.

24. Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato 'yan'uwansa da aminansa.

25. Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.

26. Amma Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma ɗan adam ne.”

27. Bitrus na zance da shi, ya shiga ya tarar mutane da yawa sun taru.

28. Ya ce musu, “Ku da kanku kun sani, bai halatta Bayahude ya cuɗanya, ko ya ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsarki, ko mai ƙazanta.

29. Saboda haka da aka neme ni, na zo, ban ce a'a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”

30. Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu'ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,

31. ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu'arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.

32. Saboda haka sai ka aika Yafa a kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus, yă sauka a gidan Saminu majemi a bakin bahar.’

33. Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”

34. Sai Bitrus ya kāda baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara,

35. amma a kowace al'umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.

Karanta cikakken babi A.m. 10