Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 4:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani a gare ni a wajen yi mini hidima.

12. Tikikus kuwa na aike shi Afisa.

13. Sa'ad da za ka taho, ka zo da alkyabbar nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

14. Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi mini mugunta ƙwarai, Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa.

15. Kai ma, ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, mummunan hauri.

16. A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.

17. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.

18. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

19. Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.

20. Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya.

21. Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.

22. Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.

Karanta cikakken babi 2 Tim 4