Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 4:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,

2. ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.

3. Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.

4. Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.

5. Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.

6. Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato.

7. Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.

8. Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.

9. Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari,

10. domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.

11. Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani a gare ni a wajen yi mini hidima.

Karanta cikakken babi 2 Tim 4