Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tim 2:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.

11. Maganar nan tabbatacciya ce,“In mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi,

12. In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi,In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,

13. In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,Domin ba zai yi musun kansa ba.”

14. Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

15. Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma'aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar gaskiya daidai.

16. Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

17. maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas,

18. waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

19. Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”

Karanta cikakken babi 2 Tim 2