Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 7:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.

11. Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.

12. To, ko da yake na rubuto muku wasiƙa, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana.

13. Saboda haka ne zukatanmu suka ƙarfafa.Banda ƙarfafa zukatanmu kuma, har wa yau mun ƙara farin ciki ƙwarai, saboda farin cikin Titus, don dukanku kun wartsakar da shi.

14. Don ko da na gaya masa cewa, ina 'yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya.

15. Ransa kuma yana a gare ku fiye da dā ƙwarai, duk sa'ad da yake tunawa da biyayyarku, ku duka, da kuma yadda kuka yi na'am da shi a cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula.

16. Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.

Karanta cikakken babi 2 Kor 7