Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 13:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.

11. Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.

12. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

13. Dukan tsarkaka suna gaishe ku.

14. Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.

Karanta cikakken babi 2 Kor 13