Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 11:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ai, ku kam, hikimarku har ta kai ga jure wa wawaye da murna!

20. Don in wani ya sa ku bauta, kukan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku.

21. Mu kam, saboda rauninmu, wane mu da yin haka!Amma ta ko yaya wani yake ƙarfin halin yin fariya, ina magana a kan ni wawa ne fa! to, ni ma sai in yi.

22. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra'ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.

23. In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.

24. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba'in ɗaya babu.

25. Sau uku aka bulale ni da tsumagu, sau ɗaya har aka jejjefe ni da dutse. Sau uku jirgi ya ragargaje ina ciki, na kwana na yini ruwan bahar yana tafiya da ni.

26. Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna , na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.

27. Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.

Karanta cikakken babi 2 Kor 11