Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 1:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.

10. Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.

11. Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.

12. Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.

13. Domin wasiƙarmu zuwa gare ku, ba ta ƙunshi wani abu dabam ba, sai dai ainihin abin da kuka karanta kuka kuma fahimta, ina kuwa fata ku fahimta sosai da sosai,

14. kamar yadda kuka riga kuka ɗan fahimce mu, cewa kwa iya yin fāriya da mu, kamar yadda mu ma za mu iya yi da ku, a ranar Ubangijinmu Yesu.

15. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.

16. Wato niyyata in bi a kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sa'an nan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya.

17. Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”?

18. Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki.

19. Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa'azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake.

Karanta cikakken babi 2 Kor 1