Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 2:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. da yake kuma ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya baƙanta masa rai ƙwarai

8. (don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa'ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci),

9. ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,

10. tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha'awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki.Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.

11. Amma kuwa mala'iku, ko da yake sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka, ba su ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji.

12. Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu,

13. suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku.

14. Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La'anannun iri!

15. Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.

Karanta cikakken babi 2 Bit 2