Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 5:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.

10. Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba.

11. Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.

12. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.

13. Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami.

Karanta cikakken babi 1 Yah 5