Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 5:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. In kuwa muka san kome muka roƙa yana sauraronmu, mun tabbata mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan.

16. Kowa ya ga ɗan'uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu'a. Saboda mai addu'ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu'a domin wannan ba.

17. Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.

18. Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.

19. Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.

20. Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.

21. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.

Karanta cikakken babi 1 Yah 5