Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 5:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.

2. Ta haka muku sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa.

3. Domin ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne.

4. Domin duk wanda yake haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta sa muka yi nasara da duniya.

5. Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?

6. Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini.

7. Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya.

8. Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.

Karanta cikakken babi 1 Yah 5