Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 4:16-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa.

17. Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari'a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan.

18. Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna,

19. Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.

20. Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan'uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba.

21. Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.

Karanta cikakken babi 1 Yah 4