Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 6:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.

8. To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.

9. Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.

10. Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.

11. Amma, ya kai, bawan Allah, ka guje wa waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimiri, da kuma tawali'u.

12. Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.

13. Na gama ka da Allah mai raya kome, na kuma gama ka da Almasihu Yesu, wanda ya yi shaida, kyakkyawar shaidar nan, a gaban Buntus Bilatus,

14. ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu,

15. wannan kuwa makaɗaicin mamallaki, abin yabo, Sarkin sarakuna. Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa.

Karanta cikakken babi 1 Tim 6