Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 6:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.

7. Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.

8. To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.

9. Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.

10. Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.

Karanta cikakken babi 1 Tim 6