Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 5:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka.

4. In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.

5. Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu'a dare da rana.

6. Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.

7. Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.

8. Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.

9. Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba,

10. wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.

Karanta cikakken babi 1 Tim 5