Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 3:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba.

9. Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.

10. Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.

11. Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.

12. Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa 'ya'yansu da sauran iyalinsu da kyau.

13. Masu hidimar da suke aikinsu sosai, suna samar wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyarsu ga Almasihu Yesu.

14. Ina sa zuciya in zo a wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa.

15. don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama'ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.

16. Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai,An bayyana shi da jiki,Ruhu ya nuna shi adali ne,Mala'iku sun gan shi,An yi wa al'ummai wa'azinsa,An gaskata da shi a duniya,An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.

Karanta cikakken babi 1 Tim 3