Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Maganar nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikkilisiya, yana burin yin aiki mai kyau ke nan.

2. To, lalle ne mai kula da ikkilisiya yă zama marar abin zargi, yă zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma.

3. Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba.

4. Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula da 'ya'yansa, su yi biyayya da matuƙar ladabi.

5. Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?

6. Lalle ne kuma, kada yă zama sabon tuba, don kada yă daga kai yă burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis.

7. Banda haka kuma, lalle ne yă zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada yă zama abin zargi, yă faɗa a cikin tarkon Iblis.

8. Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba.

9. Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.

10. Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.

11. Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.

Karanta cikakken babi 1 Tim 3