Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 1:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.

6. Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.

7. Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.

8. To, mun san Shari'a aba ce mai kyau, in mutum ya yi aiki da ita yadda ya wajaba,

9. yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,

10. da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan,

11. bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.

12. Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa,

13. ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.

14. Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu.

15. Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.

16. Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.

17. Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.

18. Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau,

Karanta cikakken babi 1 Tim 1