Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 3:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka, da muka kasa daurewa, sai muka ga ya kyautu a bar mu a Atina mu kaɗai,

2. muka kuma aiki Timoti ɗan'uwanmu, bawan Allah kuma na al'amarin bisharar Almasihu, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku a kan al'amarin bangaskiyarku,

3. don kada kowa ya raurawa a cikin tsananin wahalar nan. Ai, ku kanku kun sani an nufe mu da haka ne.

4. Domin dā ma sa'ad da muke tare, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha wahala. Haka kuwa ya auku, kamar yadda kuka sani.

5. Saboda haka, ni ma da na kasa daurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famarmu kuma yă zama banza.

6. Amma ga shi, a yanzu da Timoti ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda kuke tunawa da mu da alheri a koyaushe, har kuna begen ganinmu, kamar yadda mu ma muke yi.

7. Saboda haka 'yan'uwa, cikin dukan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya a game da ku, albarkacin bangaskiyarku.

8. A yanzu kam a raye muke, in dai kun tsaya ga Ubangiji.

9. Wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, a kan matuƙar farin cikin da muke yi a gaban Allahnmu ta dalilinku!

Karanta cikakken babi 1 Tas 3