Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 2:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. 'Yan'uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,

15. waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane,

16. suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.

17. Ya ku 'yan'uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki.

18. Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana.

19. Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?

20. Ai, ku ne abin taƙamarmu, da abin farin cikinmu.

Karanta cikakken babi 1 Tas 2