Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 7:14-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake yake a wajen matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake take a wajen mijinta. In ba haka ba, zai zamana 'ya'yanku ba masu tsarki ba ne, amma ga hakika masu tsarki ne.

15. In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.

16. Ke mace, ina kika sani ko za ki ceci mijinki? Kai miji, ina ka sani ko za ka ceci matarka?

17. Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.

18. Duk wanda Allah ya kira, wanda dā ma yake da kaciya, to, kada yă nemi zama marar kaciya. Wanda kuwa ya kira yana marar kaciya, to, kada yă nema a yi masa kaciya.

19. Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala kome, sai dai kiyaye umarnin Allah.

20. Kowa yă zauna a maƙamin da Allah ya kiraye shi.

21. In ya kira ka kana bawa, kada ka damu. In kuwa kana iya samun 'yanci, ai, sai ka samu.

22. Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai, 'yantacce ne na Ubangiji. Kuma, wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu.

23. Da tamani aka saye ku. Kada fa ku zama bayin mutane.

24. To, 'yan'uwa, duk halin da aka kira mutum a ciki, sai yă zauna a kai, yana zama tare da Allah.

Karanta cikakken babi 1 Kor 7