Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 5:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ana ta cewa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ba a yi ko a cikin al'ummai, har wani yana zama da matar ubansa.

2. A! Har kuwa alfarma kuke yi! Ashe, ba gwamma ku yi baƙin ciki ba, har a fitar da wanda ya yi wannan mugun aiki daga cikin jama'arku?

3. Ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan, kamar ma ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijinmu Yesu.

4. Sa'ad da kuka hallara, ruhuna kuma yana nan, da kuma ikon Ubangijinmu Yesu,

5. sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don yă hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.

6. Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa?

7. Ku fitar da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, domin hakika an raba ku da yistin, da yake an riga an yanka Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa, wato, Almasihu.

8. Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.

Karanta cikakken babi 1 Kor 5