Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 2:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye.

3. Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai.

4. Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,

5. kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.

6. Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba.

7. Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu.

8. A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba.

9. Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,Kunne bai taɓa ji ba,Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”

10. mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah.

Karanta cikakken babi 1 Kor 2