Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 16:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.

11. Kada fa kowa yă raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo a gare ni, domin ina duban hanyarsa tare da 'yan'uwa.

12. Ga zancen ɗan'uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don yă zo wurinku, tare da saurar 'yan'uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa'ad da ya ga ya dace.

13. Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.

14. Duk abin da za ku yi, ku yi shi da ƙauna.

15. To, 'yan'uwa, kun sani fa jama'ar gidan Istifanas su ne nunan fari a ƙasar Akaya, sun kuwa ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima.

16. Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda suke abokan aikinmu da wahalarmu.

17. Na yi farin ciki da zuwan Istifanas, da Fartunatas, da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku.

18. Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.

19. Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.

20. Dukan 'yan'uwa suna gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

21. Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna.

22. Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!

23. Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku.

Karanta cikakken babi 1 Kor 16