Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah.

10. Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.

11. To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa'azi, ta haka kuma kuka gaskata.

12. To, da yake ana wa'azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu?

13. In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan.

14. In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa'azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce.

15. Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu.

16. Don kuwa in ba a ta da matattu, ashe, Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan.

17. In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku.

18. Ashe, waɗanda suka yi barci a kan su na Almasihu, sun hallaka ke nan.

19. Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi.

20. Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15