Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 14:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa.

5. To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.

6. To, 'yan'uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba?

7. In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?

8. In ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?

9. Haka ma yake a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahimta ba, yaya wani zai san abin da ake faɗa? Kun yi magana a banza ke nan!

10. Hakika akwai harsuna iri iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma'ana.

11. In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni.

12. Haka ma yake a gare ku. Tun da yake kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikkilisiya.

13. Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yă yi addu'a a yi masa baiwar fassara.

Karanta cikakken babi 1 Kor 14