Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 14:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Wato, ashe, harsuna a kan alamu suke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa domin masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba.

23. Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba?

24. In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa,

25. asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.

26. To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.

27. In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara.

28. In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci.

29. Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar.

Karanta cikakken babi 1 Kor 14