Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 12:16-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba.

17. Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?

18. Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa.

19. Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?

20. Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.

21. Ba dama ido yă ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai yă ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.”

22. Ba haka yake ba, sai ma gaɓoɓin da ake gani kamar raunana, su ne wajibi,

23. gaɓoɓin jiki kuma da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mukan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓinmu marasa kyan gani, akan ƙara kyautata ganinsu.

24. Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa,

25. kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya.

26. Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.

27. To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.

28. A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri.

29. Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu'ujizai ne?

30. Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara?

Karanta cikakken babi 1 Kor 12