Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 12:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa.

15. Da ƙafa za ta ce, “Da yake ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce,” faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba.

16. Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba.

17. Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?

18. Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa.

19. Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?

20. Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.

Karanta cikakken babi 1 Kor 12