Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 2:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah.

5. Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,

6. Domin a tabbace yake a Nassi cewa,“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”

7. A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,“Dutsen da magina suka ƙi,Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”

8. Da kuma,“Dutsen sa tuntuɓe,Da fā na sa faɗuwa.”Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.

9. Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.

10. Dā ba jama'a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama'ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.

11. Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.

Karanta cikakken babi 1 Bit 2