Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 1:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,

5. wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.

6. A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.

7. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.

8. Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,

9. kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.

10. Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto,

11. suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.

12. An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.

13. Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.

14. Ku yi zaman 'ya'ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha'awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku.

Karanta cikakken babi 1 Bit 1