Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 1:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,

2. su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.

3. Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

4. mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,

5. wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.

6. A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.

7. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.

Karanta cikakken babi 1 Bit 1