Sheba da Dedan, da 'yan kasuwar Tarshish, da dukan garuruwa za su ce maka, ‘Ka zo kwasar ganima ne? Ko ka zo ka tattaro rundunarka don ka yi waso, ka kwashe azurfa da zinariya, da bisashe, da dukiya, ka kwashe babbar ganima?’